Namijin Dare/Macen Dare
Tun farko yana da muhimmaci mu san menene a ke nufi da Namijin dare ko Macen dare? Namijin dare na nufin Jinnul-Ashiƙ wanda ke nufi da wata hulda ta soyayya dake aukuwa a tsakanin Dan Adam da Iska.
Idan ka yi dubi zuwa tarihin Hausawa za ka ga cewa kafin addinin Musulunci ya samu karɓuwa a ƙasar Hausa suna da tarihin hulɗa da Iskoki. A da, ƴan bori da bokaye da Malaman tsibbu suke cin karen su ba babbaka a kan sha,anin hulɗa da iskoki hanka yasa ake samun aljanu na gado, da waɗanda aka tura wa mutum ta hanyar sihiri da kuma gamau (Wadanda suka hadu da mutun kan hanya, juji ko a bandaki).
Ma'anar Namijin Dare/Macen Dare
Namijin dare ko Macen dare wani nau'in iska ne daga cikin iskoki wanda ke auren mace 'ƴar Adam yana saduwa da ita (jima'i), ko kuma iska mace ta auri mutum dan Adam ta rinƙa saduwa da shi ta hanyar mafarki ko a farke, musamman cikin dare. Irin wannan saduwa tana haddasa cututtuka ga jiki ko zuciyar dan Adam. Malaman ruƙiyya na kiran irin wannan iska da sunan 'Aljanin/Aljanar soyayya'.
Ga kaɗan daga cikin dalilan da kan jawo shigar Namijin dare ga mace su ne:
Tsiraitar da al'aura ga mace ko namiji cikin gida, kamar mace ta tsiraita zindir ko ta sanya tufafi maras kauri, kuma ta zo ta tsaya gaban madubi, tana mamakin kyawon kanta, idan aka yi rashin sa'a aljanin soyayya yana kusa, sai ya yi sha'awar ta, kuma son ta ya kama shi sai ya shige ta
Idan mace ko namiji suna kwantawa a tsiraice a waje, misali lokacin bazara, kuma ba su ambaci sunan Allah ba, Namijin dare ko macen dare kan yi sha'awarsu, kuma su shige su.
Idan mace ko namiji na shiga ban-daki wajen wanka a tsiraice, ko shiga ruwa (gulbi ko kududdufi) wajen wanka a tsiraice kuma ba a ambaci sunan Allah ba. Namijin dare ko macen dare kan samu saukin shigarsu kuma ya aure ta ko ta aure shi.
Idan mace na bayyanar da kawarta a titi ko bainar jama'a, Namijin dare na iya kai mata hari.
Idan mutum na saduwa da iyali ba tare da ambaton sunan Allah ba, shaidanin aljani kan samu damar shiga jikinsa ko jikin iyalin.
Idan mutum ya sadu da iyalinsa alhali tana haila namijin dare zai riga shi gare ta.
Ga kaɗan daga cikin Alamomin da a ke gane Mace na da Namijin dare;
1- Ta riƙa jin matsanancin ciwon kai kullum.
2- Ta riƙa samun yawan faduwar gaba.
3- Ta riƙa jin ba ta son zama gidan miji, ko jin bacin rai wanda babu dalili.
4- Ta riƙa jin ciwon kwankwaso ko kuncin kirji.
5- Ta riƙa jin ciwon mara a kai-a kai.
6- Isasshen Ta riƙa fama da rashin barci ko yawan farkawa cikin dare, kuma cikin tsoro.
7- Rashin tsayar da miji idan ba ta da aure, kuma ga mabida na zuwa wurinta.
8- Daɗewa ba ta yi aure ba idan budurwa ce.
9- Yawan mutuwar aure, ta kasa tsayawa ga miji daya. Idan aka ga haka ga mace, kari da wasu alamomi, to ana tuhumar tana tare da namijin dare.
10- Yawan mutuwar aure, ta kasa tsayawa ga miji daya. Idan aka ga haka ga mace, kari da wasu alamomi, to ana tuhumar tana tare da namijin dare
11- Ta zama mai wabi (yawan mutuwar 'ya'ya tun suna kanana tsakanin shekara daya zuwa biyar).
12- Yawaitar samun bari (zubewar ciki), daga wata daya zuwa uku
13- Yawan zubar jinin haila a kai a kai, musamman lokacin da namijin dare ita. zai sadu da
14- Rashin haihuwa.
MAGANIN NAMIJIN DARE
1- Domin magance matsalar na Namijin dare yana da muhimmaci a yawaita karatun Al-Kur’ani mai girma a kuma dage da azkar safe da yamma.
2- Ana rubuta ayatul kursiyyu 41, suratul Yasin kafa ɗaya zata sha tsawon kwana bakwai ko kuma a rinƙa iya karantawa ana tofawa ana sha kullum. Za a samu lafiya da yardan Allah.
3- Ana samun ganyen sarkuwan sauro a busar da shi a haɗa da man-gelu a cakuɗa sosai a rinƙa yin Hayaƙi da shi safe da yamma za a rabu da namijin dare. Insha Allah.