ASRAR NA SURATUL YASIN
Da farko dai suratun Yasin an saukar da ita ce a Makka tana da adadin ayoyi (83), kalmomi 729. Suratul Yasin tana da fa’idoji masu yawan gaske kuma akwai ruwayoyi da suka zo dake nuni a kan falalar wannan sura mai albarka. Ga kaÉ—an daga ciki:
An karÉ“o daga Imam Sadiq (A.S) ya ce: Kowane abu yana da zuciya, kuma zuciyar Al-Ƙur’ani ita ce Suratul-Yasin wanda ya karanta suratul Yasin kafin ya yi barci ko da rana kafin ya yi tafiya, to a ranar zai kasance cikin waÉ—anda ake ba wa kariya ake azurtawa har zuwa Marece (Yamma). Wanda ya karanta da dare kafin ya kwanta barci, Allah zai wakilta Mala’iku da za su rinÆ™a kare shi daga sharrin ShaiÉ—an la’antacce, da kuma duk wata musiba, kuma idan ya mutu a wannan dare Allah zai shigar da shi aljanna, kuma Mala’iku dubu talatin (3,000) ne za su halarci yi masa wanka dukkansu za sun rinÆ™a nema masa gafaran Allah, kuma za su raka shi har Æ™abarinsa suna nema masa gafara…..’’.