DOMIN SAMUN SOYAYYA DA MALLAKA MAI KARFI



ADDU’AR MALLAKA DA SOYAYYA.


Kamar yadda muka sanin a zamantakewa musamman ma na Aure akwai buƙatar soyayya matuƙar gaske,kai ma ana iya cewa itace tubulin ɗorewan aure da zuriya ta gari. Kuma harwayu yana daga cikin abubuwan da muke fama da shi wato matsalolin da ake samu ta wannan bagare, kama daga lalacewar aure saboda ƙarancin soyayya wanda hakan ke haddasa ɗaiɗaicewan zuriya da kuma rashin tarbiyya a cikin al'umma.

Wannan matsala ta karancin soyayya ta kan kai ga wasu su faɗa cikin aikata ayyuka na saɓon Allah kamar zuwa wajen bokaye da masu sihiri duka dai domin samun soyayya da zaman lafiya a tsakaninsu da abokan zaman zu. 

Wanda kamar yadda muka sani yin hakan Haramun ne a musulunci kuma bai kamata ba mutun musulmi ya rinƙa zuwa wajen bokaye domin samun mafita daga matsalar da yake ciki ba.

Musulunci ya ƙarfafamu da yin addu’a haka kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad (Salallahu Alaihi wa alihi Wasallam) ya nusar da mu akan muhimmancin yin addu’a.

Kuna iya samun karanin bayani ta hanyar dannan wannan link dake kasa👇

ADDU'AR SOYAYYA DA MALLAKA

Ga addu’ar da ake karantawa domin samun soyayya da mallaka:


بسم الله الرحمان الرحيم اللهم صل على محمد وآل محمد

اللًهلُم يا واحد يا أحد يا فرد يا صمد يا علي يا عظيم سخرلي ..(اسم الزوج)... كما سخرت الريح لسليمان وألن قلبه كما ألنت كما الحديد لداود وأذله كما أذللت فراعون لموسى واجعل ذلك في طاعتك فإنه لاَ يَنطِقُ الشَّهَادَةَ َ إِلاَّ بِذنِكَ.

اللهم إني أسألك باسمك الأعظم الأجل الأعز الأحد الصمد أن تصلي وتسلم على نبينك محمد وأن توفق بيني وبين ..... وأن تجمع بيننا علي خير اللهم أصلح ذات بيننا وأعذنا من الشيطان الرجيم وأبعد عنا شرَّ القلوب الحاقدة والعيون الحاسدة اللهم أقر عيني هِدايَتُهُ  وصَلَاحُهُ والتقواه وأرزق كل من حب وودُ الآخروجمل كل منا في نظر الآخر وجعل كل عون للآخر على طاعتك اللهم سخره لي بحولك وقدرتك فأنت القادر على ذلك وحدك اللهم لا تسلط علينا من لا يخافك ولا يرحمنا.  

Tanbihi: Wuraren da aka sanya baka wato wadannan alamar kamar haka .....(  ) ...  wanda ke cikin addu'ar za ambaci sunan wadanda ake so a samu soyayya da kaunarsa.

Domin samun ƙarin bayani kuna iya tuntuɓarmu ta WhatsApp ±2347062014111

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post