Wannan addu’ar ana yinta ne domin neman wata ƙujerar mulki ko shugabanci ko sarauta haka kuma ana yinta domin samun jama’a a cikin harkar kasuwanci ko sana’a. Ana karanta wannan ayar da zamu kawo a ƙasa sau ƙafa 11, ga ayar kamar haka:
قُلِ ٱللَّهُمَّ مَٰلِكَ ٱلۡمُلۡكِ تُؤۡتِي ٱلۡمُلۡكَ مَن تَشَآءُ وَتَنزِعُ ٱلۡمُلۡكَ مِمَّن تَشَآءُ وَتُعِزُّ مَن تَشَآءُ وَتُذِلُّ مَن تَشَآءُۖ بِيَدِكَ ٱلۡخَيۡرُۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ .
تُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَتُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِۖ وَتُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَتُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّۖ وَتَرۡزُقُ مَن تَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ .
Bayan ka karanta ayar da muka kawo a sama ƙafa 11 sai kuma ka karanta wannan addu’ar dake kasa ƙafa ɗari da goma sha ɗaya (111). Ga ayar nan a kasa:
وَتَرۡزُقُ مَن تَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ
Idan ka kammala sai ka ambaci buƙatarka za ka yi ta yin wannan addu’ar tsawon kwana sha ɗaya.