LADUBBAN SADUWA A DAREN FARKO



Jima’i

Saduwa ce tsakanin miji da mata da nufin samun biyan bukatar sha'awa ko kuma da nufin samun haihuwa. Masana sun tabbatar da cewa, jima’i na kara dankon aure, musanman idan kowane daga cikin ma'uaratan na samun biyan bukatarsa ta sha'awa. Don haka dole ne a yi magana a kan wannan domin a san shi a kuma san matsalolin da ke tare da shi, domin daga cikin matsalolin akwai abin da ke hana ko shi namiji ko ita macen samun damar yin jima'in yadda ya kamata, sanin wannan ne zai bashi damar neman magani domin ganin ya magance wannan matsalar. 

 LADUBBAN SADUWA A DAREN FARKO:
 Ango da amarya su tsara yadda za su fara soyayyarsu ta zaman aure ta yadda kowanensu zai kasance yana cikin natsuwa, wadansu kan sa lokacin jima'insu ya kasance bayan cin abin ci, wasu ko da yamma, wasu da dare Amma lokacin da ya fi shi ne lokacin da za a samu natsuwa kuma a dade musamman a daren farko. Ba a so a abin ci da yawa ko a sha ruwa ko wani abin sha da yawa, in har ana so a ci ko a sha kafin jima'i to kar a sha da yawa kuma kar a ci abu mai nauyi. Domin Annabi (s.a.a.w) yana cewa: "Ango ya shiga dakin amaryarsa da nono”. A samu wurin da babu hayaniya kuma ba a tunanin wani zai shigo. A bi hanyar da za a tayar wa juna sha'awa, ta shafar jikin juna ko a kama hannu a dora kan fuska da sauransu domin tayar da sha'awa. Ku zabi yadda kuke so ku kwanta ko ta rigingine ke amarya ta yi goho ko abin da yayi kama da haka. Kada mai gida ya dauka shi kadai ke da haƙƙin jima'i dukansu ma'auratan na da haƙƙin jima'i don haka kowannensu na iya jagoranta. Idan ya kasance ango na da babba azzakari ta yadda tsawon ko kaurin azzakari ya wuce ƙima, sai ya yi amfani da dubarun da ba zai cutar da marya ba.

 MATSALAR ƊAUKEWAR NI'IMA
 Yawancin ɗaukewar ni'ima na faruwa ne ta dalilai kamar haka:- Cutuka da ake dauka ta hanyar jima'i (S.T.D) ko kuma Cutukan mahaifa (womb disease). Matsananciyar jinya, musamman irin su cutar zazzabin cizon sauro (malaria). Rashin samun isasshen abin ci Shafar baƙin aljani jinnul Ashiƙ) Rashin kwanciyar hankali tsakanin ma'aurata Shan magungunan asibiti masu alaƙa da zuciya (akwai nau'ukan maganin asibiti da idan mace tana amfani da su za ta samu bushewar farji) hakan na iya kore samuwar ni'ima wajen jima'i don haka sai a kiyaye. Idan kuma haka ya faru ne sanadiyar daukan cuta a wurin jima'i ko wata cuta ta daban sai a nemi hanyar magancewa domin dawo da ni'imar da aka rasa. Idan ta dalilin rashin kwanciyar hankali ne ne zamantakewar aure ko rashin abinci mai gina jiki, to da zarar an sami canjin yanayi sai ita ma ni'imar ta dawo. Idan kuma ta dalilin shan wasu kwayoyi ne, to da zarar ta daina sha sai ta ga canji. Haka nan ma za a iya canza nau'in maganin da ake sha domin samun daidaituwar ni'ima wajen yin jima'i. Idan kuwa ta dalilin shafar aljani ne, za a iya ganin alamun shafar aljani a tare da matar, kamar su yawan ɓacin rai, yawan firgici, miyagun malankai, yawan Ciwon kai da sauransu. A kan samu cewa wasu matan aljani na saduwa da su, idan haka na faruwa sai na ƙona aljanin ne sannan za a samu zaman lafiya, da dawowar ni'imar jima'i a tare da ita. Idan namiji na saurin kawo maniyi da zaran ya fara jima’i, to ya nemi dabino ya bare ya cire yayan na ciki ya hada da nonon ya bari ya kwana har sai ya fara tsami, sai ya rika wanke gabansa da shi domin samun daidaito wurin fitar maniyi a lokacin jima’i.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post